Kudurori kan dokar haraji guda hudu da Shugaba Bola Tinubu ya aike wa Majalisar Wakilan Najeriya sun tsallake karatu na biyu.
Hakan na zuwa ne watanni 6 bayan da Shugaba Tinubun ya aikewa Majalisar Dokokin kasar sakamakon shawarwarin da kwamitin manufofin kudi da sauye-sauyen dokar haraji karkashin jagorancin Taiwo Oyodele ya bayar
A yau Laraba, Majalisar Wakilan Najeriya ta fara mahawara a kan kudurorin dokar haraji guda 4 da Shugaba Bola Tinubu ya aike mata a shekarar data gabata.
Kudurorin sun hada dana dokar harajin Najeriya ta 2024 da kudirin gudanar da haraji dana kafa hukumar tattara harajin Najeriya da kuma na kafa hukumomin tattara haraji na hadin gwiwa.
Sabbin kudurorin harajin sun janyo kace-nace da suka da tsananin adawa daga bangarori da dama, ciki harda gwamnonin jihohin arewacin kasar da ‘yan siyasa daga bangaren adawa da suka nemi a janye su daga gaban majalisar dokokin kasar.
Yayin zaman majalisar na yau Laraba, galibin masu mahawarar sun goyi bayan kudurorin, saidai dan majalisa, Sada Soli, na fargabar cewar wasu sassa na sabbin kudurorin na iya cin karo da kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999.
Dandalin Mu Tattauna