Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dattawan Najeriya Ta Fara Zaman Sauraron Ra’ayin Jama’a Kan Kudurorin Haraji

Zauren majalisar dattawan Najeriya (Facebook/Nigerian Senate)
Zauren majalisar dattawan Najeriya (Facebook/Nigerian Senate)

Tattaunawar za ta mayar da hankali ne akan kudurin kafa hukumomin haraji na hadin gwiwa dana hukumar tattara haraji ta Najeriya, yayin da za’a tattauna akan kudirin gudanar da harkar haraji a Najeriya da kuma na dokar harajin Najeriya.

A yau Litinin, Majalisar Dattawan Najeriya ta shirya tsaf domin fara zaman sauraron ra’ayin jama’a na yini 2 a kan kudurorin dokar haraji a wani bangare na kokarin yiwa tsarin harajin kasar garanbawul tare da bunkasa samun kudin shiga.

Zaman jin ra’ayin jama’ar da kwamtin majalisar akan harkokin kudi ne ya shirya zai kunshi tuntuba da manyan jami’an gwamnati da kuma muhimman masu ruwa da tsaki 71.

Tattaunawar za ta mayar da hankali ne akan kudurin kafa hukumomin haraji na hadin gwiwa dana hukumar tattara haraji ta Najeriya, yayin da za’a tattauna akan kudirin gudanar da harkar haraji a Najeriya da kuma na dokar harajin Najeriya.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG