JOS, NIGERIA —
A shirin Zamantakewa na wannan makon mun tattauna ne kan halin da tsofaffin jami'an hukumar gidan gyara hali suka shiga, bayan ritaya daga aiki.
Kundin tsarin mulkin Najeriya dai ya kayyade shekaru talatin da biyar ne na aikin gwamnati ko shekaru sittin da haihuwa don ma'aikacin gwamnati ya huta daga aiki.
Wasu dai daga cikin tsofaffin jami'an hukumar gidan gyara hali sun ce suna karbar Naira dubu ishirin ne kachal a matsayin kudin fansho a karshen kowace wata.
Saurari cikakken shirin da Zainab Babaji ta gabatar:
Dandalin Mu Tattauna