Barrister Tanko Beji ne aka bayyana cewa ya lashe zaben shugaban jam'iyyar na jihar Neja ba tare da wani abokin hamayya ba.
Amma masu adawa da yadda aka gudanar da zaben sun kira taron manema labarai inda suka zargi tsohon gwamnan jihar Injiniya Abdulkadiri Kure da yin kakagida tare da hana wasu 'ya'yan jam'iyyar takardun shiga takarar, zargin da ya musanta yana cewa shi dan jama'iyya ne bashi da wata madafar iko.
Tsohon mai bada shawara akan sha'anin shari'a ga jam'iyyar ta PDP a jihar Barrister Zubairu Ishata Abdullahi shi ya yiwa manema labarai bayani akan lamarin. Yace ba zabe aka yi ba. Tsohon gwamnan jihar Injiniya Kure shi ne ya sawa wasu albarka, ya basu takardun neman zabe su cike kana ya kaisu zaben domin a ce an zabesu.
Shi ma tsohon sakataren gwamnatin jihar Yahaya Idris Indako ya bayyana matsayinsu. Yace sun kai kara kan zaben. Zabe sai an bar mutane dake neman mukami sun tsaya za'a ce an yi zabe amma a wannan babu wanda aka bari sai mutanen da Kure ya kawo.
To saidai sabon shugaban jam'iyyar Barrister Tanko Beji yace zai yi kokarin hada kan 'ya'yan jam'iyyar domin cigabanta.
Ga karin bayani.