Wannan darewar ta biyo bayan rikicin da wasu shugabannin jam'iyyar suka shiga akan zargin cewa wasunsu sun yi awan gaba da kayan zabe da aka turo jihar.
Yayinda yake karban malaman zaben da uwar jam'iyyar ta turo jihar domin gudanar da zabukan shugaban jam'iyyar a jihar Chief Jonah Joel Madakai ya nuna bacin ransu ne tare da zargin cewa tsohon hadimin shugaban kasa Goodluck Jonathan wato Barrister Ali Gulak shi ya yi awan gaba da kayan zaben.
Amma Barrister Ali Gulak ya musanta zargin. Yace uwar jam'iyyar ta bukaci a biyata nera miliyan tara kafin ta aika da kayan zaben amma shi ya shaidawa shugaban jam'iyyar cewa mutanensu ba zasu iya fitar da kudin ba nan take. Ya roka a bada kayan bayan an sayar sai a maida masu kudin. Dalili ke da uwar jam'iyyar tace idan zai dauki alkawarin biyan kudin ya rubuta masu su bashi kayan. Haka ko ya yi.
Yace da aka bashi takardun zaben sai ya mikawa wadanda jam'iyyar zata aika Adamawa su gudanar da zaben. Bayan awa uku Joel Madaki ya je neman kayan aka yi masa bayanin abun da ya faru.
Shugaban tawagar jami'an zaben yace zasu gudanar da zabukan tun daga matakin anguwanni har zuwa jiha, sai sun gama kakaf tsakininsu da Allah.
Ga karin bayani.