Rikicin ya kanno kai ne biyo bayan dakatar da shugabannin jam'iyyar reshen jihar da uwar jam'iyyar ta kasa ta yi.
To saidai shugabannin sun ce hakan ba zai yiwu ba. Ita uwar jam'iyyar ta kasa ta bukaci shugabannin su koma jefe guda domin a samu a gudanar da sabon zaben shugabannin.
A taron manema labarai shugaban jam'iyyar Chief Joel Madaki ya zargi wasu shugabannin jam'iyyar da zama kanwa uwar gami, wato masu tada hargitsi a jam'iyyar. Chief Madaki yace shi ne shugaban jam'iyyar a jihar Adamawa tare da zargin cewa akwai wasu mutane cikinsu da aka biyasu su ruguza jam'iyyar. Saboda haka su ba zasu bari a wargaza masu jam'iyya ba.
Duk da wannan rikicin na jam'iyyar hukumar zabe mai zaman kanta ta sake jaddada shirinta ta gudanar da zaben kananan hukumomi watan gobe. To saidai ita hukumar, tace gwamnatin jihar na tunanen dage zaben zuwa wani lokaci.
Alhaji Isa Shattima shugaban hukumar zaben yace su sun shirya tsaf domin gudanar da zaben. Yace sun riga sun bada jadawalin zaben kuma sun ba 'yan siyasa su fara neman zabe tare da fidda wadanda zasu tsaya masu. Yace shi bai san batun kafawa kananan hukumomi kwamitin riko ba, amma ya sa ranar da za'a yi zabe.
Ita ma jam'iyyar APC ta musanta zargin neman canza jadawalin zaben. Tace ashirye take ta shiga zaben kuma zata amince da sakamakonsa.
Ga karin bayani.