A firar da Alhaji Shehu Musa Gaba wani jigo a jam'iyyar PDP ya yi da Muryar Amurka yace sake mayarda shugabancin jam'iyyar tasu zuwa arewa maso gabas ba zai haifar masu da mai ido ba a zaben 2019.
A cewarsa yin hakan manuniya ce ga jam'iyyar da ma kasa cewa dan arewa ba zai tsaya takarar shugaban kasa ba a zabe mai zuwa.
Yace rudu ya riga ya shiga jam'iyyar. Yace 'yan kwamitin da aka sa su zauna maimakon su duba abun da zai yiwa kasar alheri sai suka yi son zuciyarsu.Abun da yakamata kwamitin din ya yi shi ne tura shugabancin jam'iyyar zuwa kudu ba arewa ba. Tunda kwamitin zartaswa na jam'iyyar ya riga ya fada cewa dan takarar shugaban kasa daga arewa zai fito, shugaban jam'iyya bai kamata ya fito daga arewa kuma ba.
Lamarin yanzu ya kawo baraka tsakanin 'yan jam'iyyar saboda haka ana kiran 'yan arewa kada su je taron kolin jam'iyyar da za'a a yi a Fatakwal. Maimakon hakan 'yan arewa su taru a Abuja su yi nasu taron domin su dauki matsaya daya.
Tun ranar da aka kafa jam'iyyar an yadda cewa shirin karba karba shi ne zai kawo zaman lafiya a kasar
To saidai mataimakin kakakin jam'iyyar Barrister Abdullahi Jalo yace batun ba haka yake ba. Yace su ma dan arewa suke son ya tsaya takara.
Ga karin bayani.