Jam'iyyar dai ta kalubali APC mai mulkin jihar Bauchi da gazawa wajen inganta rayuwar 'yan Najerita, musamman 'yan jihar.
Alhaji Salisu Barau tsohon kwamishanan labarai a gwamnatin Isa Yuguda, gwamnatin PDP da ta shude a jihar ya yi karin haske akan makasudin taron. Yace sun kira taron ne domin su nunawa duniya yayinda ake gutsuri tsomi a jihar cewa gwamnati ba karya ba ce gaskiya ce.
Yace su sun yiwa jihar Bauchi ayyuka.Kuma duk dan jihar ganao ne , jinau ne kuma yana ganin abun dake faruwa yanzu a jihar. Matsalolin rashin albashi ma kadai ya isa. Yace gwamna Isa Yuguda a kusan shekaru takwas da ya yi yana mulki ana biyan albashi kan kari.
Akan zargin cewa gwamnatin PDP ce ta jefa kasar cikin matsalolin da ake fuskanta yanzu sai Alhaji Barau yace babu dan adam da zai ce bashi da matsala. Idan wadan can matsalolin suka jawo faduwarsu to yanzu talakawa sun gani. Yace yau me ma'aikaci da manomi da talakan kasa ke ciki?
Ya cigaba da cewa a jihar Bauchi gwamna Yuguda ya yi hanyoyi,asibitoci, filin jirgin sama, asibitin koyaswa, tare da kawo taki kafin damina ta fadi.
Kakakin gwamnan jihar Bauchi na yanzu ya mayarda martani. Sabo Muhammad yace 'yan Najeriya ba zasu manta da irin gallazawar da PDP ta yi masu ba. Jam'iyyar ta yi sakaci da tsaro da watanda da aka dinga yi da dukiyar kasar. Yanzu gwamna M.A. Abubakar yana kokarin gyara kurakuran PDP da rashin kishin jiha da ta shuka da kuma sakaci da ta yi da tattalin arzikin jihar. Gwamnatin PDP ta tafi ta barwa jihar bashin da ya haura nera biliyan 125.
Ga karin bayani.