'Yan adawana na zargin cewa sayen katunan zabe da jam'iyyar PNDS ke yi alama ce ta shirya magudin zabe a zaben ranar 21 ga wannan watan.
Malam Jinna Abdullahi jigo a jam'iyyun adawa ya karawa Muryar Amurka bayani dangane da abubuwan da suka gano. Yace katunan zabe ba'a bayarwa sai da shaida amma su 'yan PNDS kwasa a keyi ana basu. Kana akwai wasu da suke saya.Ya bada misalan garuruwan da ake sayar da katunan.
Da yake mayarda martani akan zargin Malam Isa na PNDS kuma dan kwamitin fafytikar neman an sake zabar jam'iyyarsa ta PNDS. Yace shekaru 15 suka yi suna mulki basu yi wani abu ba sai sace sace da magudi amma yanzu da suka ga aiki suna shata karerayi. Su ba zasu yi abun da 'yana adawa suka yi lokacin da suke mulki ba. Yace su basu bukatar yin magudi ko cin hanci da rashawa.
Amma 'yan adawa suna cigaba da tattara bayanan da zasu gabatar gaban kotu saboda a baya bayan nan an gano 'yan Nijar fiye da miliyan daya da ba zasu samu kada kuri'a ba sakamakon yin rajista ta hanyar shaidu maimakon samun kati.
Hukumar zabe dai na cigaba da fadakar da jama'a kan inda zasu kada kuri'a da yadda zasu yi. Haka ma hukumar ta fitar da sunayen wadanda suka cancanta su kada kuri'u a yanar gizo.
Ga karin bayani.