Zaben ya sami tsallakewa da kuri’un ‘yan majalisa kimanin 499, a yayin da guda 16 suka zura idanu ba tare da zaben ba, wasu ‘yan majalisar da dama kuwa kauracewa zaben raba gardamar suka yi.
Kwaskwarimar ta haifar da wa’adin mulki biyu sau biyu ga shugaban kasa, wanda gyara ne akan kwaskwarimar shekarar 2008, da ta ba Shugaba Abdulaziz Bauteflika damar sake tsayawa takarar wasu wa’adin mulki har sau biyu.
Haka kuma Shugaban kasar ne zai bada sunan Firaminista daga mafiya rinjaye a Majalisa. ‘Yan adawa sun ce kwaskwarimar ta kunshi abubuwa masu ma’ana. Amma sun ce ana bukatar sake kwaskwarima don takaita karfin ikon jam’iyyar Shugaba Abdulaziz ta FLN mai mulkin kasar.