Zuwa yamma, hukumomi sun tabbatar da mutuwar akalla 54 daga cikin wadanda su ka je nemar shiga sojan gwamnati, sannan wasu kuma 70 sun samu raunuka, a wannan harin wanda shi ne mafi muni a wannan shekarar a kasar ta Larabawa mai iyaka da ruwaye. Kafar labaran Faransa ta ruwaito majiyoyin asibitin wurin na cewa wadanda su ka mutu sun kai 71, wadanda su ka kuma ji raunuka sun kai 98.
Hukumomi sun ce an auna wata makaranta ne, inda masu nemar shiga soja gwamnatin Shugaba Abd-Rabbu Mansour Hadi ke rajista don fara samun horon soji.
Shaidu sun ce maharin ya shiga ginin makarantar ne ta wajen bin bayan wata motar daukar kaya, mai dauke da abincin da za a baiwa masu shirin shiga sojan. Kungiyar likitocin agaji na MSF sun ruga da akasarin wadanda su ka ji raunin zuwa asibitocin wurin, wadanda abin ya fi karfinsu.
Jim kadan da fashewar, ISIS ta fitar da wata sanarwa, wadda aka yada ta kafar labarai ta Amaq mallakarta ta na mai daukar nauyin kai harin.