Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Kasashen Turai Sun Rufewa Musulmai Yan Gudun Hijira Kofa


A jiya Lahadi ne shugabar Jamus, Angela Markel, tace ba zata yiyu ba ace wasu kasashen dake cikin kungiyar Tarayyar Turai su kullewa ‘yan gudun hijira kofa domin kawai suna musulmai.

Tace tilas ne kowa ya taka nasa rawar da ya dace ya taka.

Shugabar tana magana ne sailin da take wa gidan talabijin na ARD jawabi.

Shugabar Markel, taci gaba da cewa abin da take ganin bai dace ba shine wasu na cewa kusan dukkan mu ne bamu son musulmi a kasar mu, ko da kuwa akwai bukatar bada aikin jin kai ko a’a, don haka tace zasu ci gaba da magana akan wannan batu.

Shugabannin kasar ta Jamus suka ce suna sa ran su baiwa yan gudun hijira da yawan su yakai dubu dari 3 damar shiga cikin kasar a cikin shekarar nan ta 2016, wadanda kuma yawancin su ‘yan kasar Afghanistan ne da Iraq, da kuma Syria, inda rayuwar su take cikin hadari sakamakon yaki da ayyukan ta'addanci da ake yi a kasashen nasu.

Markel tace tana son a samar tsarin raba dai-dai tsakanin kasashen 28 da suke cikin wannan kungiyar na wadanda zasu zamo ‘yan gudun hijira.

Yanzu haka dai wasu daga cikin ‘yan kungiyar ta Tarayyar Turai musammam wadanda suke daga gabashin Turan sun ki yarda da wannan tsarin na karban ‘yan gudun hijira daga gabas ta tsakiya yayin da wasu kuma suka ki amincewa da tsarin raba dai-dai.

Musali shugaban Chech, wato Prime Ministan Bohauslav Sabotka, ya fada a cikin satin data gabata cewa shi baya son tawagar musulmai da yawa kasar sa saboda matsalolin da suke gani, yace ya rage ga kungiyar tarayyar Turai din data yanke hukuncin adadin ‘yan gudun hijira nawa zata karba gaba daya.

XS
SM
MD
LG