Najeriya ta samo ranchen dala bilyan 1.1 daga bankin raya kasashen Afirka (AfDB) domin samar da lantarki ga mutane miliyan 5 kan nan da karshen 2026.
A cewar mashawarcin shugaban Najeriya akan harkokin yada labarai da tsare-tsare, Bayo Onanuga, Bola Tinubu ya bayyana hakan ne a jawabin da ministan lantarkinsa, Adebayo Adelabu, ya gabatar yayin kammala taron yini 2 a kan samar da makamashi a Afirka mai taken: “mission 300 Africa Energy Summit” da ya gudana a birnin Dar Es Salaam na kasar Tanzania.
Tinubu ya kara da cewa dala miliyan 200 da AfDB ya zuba a Najeriya domin aikin samar da lantarki zai sama wa mutane dubu 500 hasken lantarki kan nan da karshen 2025.
“Ni (Tinubu) ya shaida wa cewa ana sa ran ranchen dala biliyan 1.1 da AfDB ya bayar ya samar da lantarki ga mutane miliyan 5 kan nan da 2026, yayin da dala miliyan 200 da ya zuba a aikin samar da lantarki a Najeriya zai samar da hasken lantarki ga mutane dubu 500 kan nan da karshen 2025.
“Wannan buri ne mai wuyar gaske, amma zamu iya cimma sa a tare,” a cewar Tinubu. A matsayina na Shugaban Najeriya, zan jajirce wajen baiwa aikin samar da lantarki fifiko.”
Dandalin Mu Tattauna