A jawabin da ya shafe mintoci sama da 60 yana yi wa 'yan Nijer albarkacin zagayowar wannan rana, Shugaba Issouhou ya bayyana cewa Nijer ta sami ci gaba a fannoni da dama.
To sai dai ra’ayoyi sun sha bamban a game da kamun ludayin Shugaban, domin a cewar Annabo Soumaila, wani kusa a kawancen jam’iyyun hamayya na FRDDR, babu wani takamaiman sauyi da aka samu a tsawon wannan lokaci.
Shugaba Issouhou Mahamadou ya bayyana cewa dimokradiyya ta kara girkuwa a tsawon shekaru 9 na gwamnatinsa, abinda ke ba ‘yan kasa damar morar ‘yancin bayyana ra’ayi ko fadin albarkacin baki, sai dai wani jami’in fafutika Abdou Elhadji Idi na cewa ba haka zancen yake ba.
Da yake maida martani akan wadannan bayanai, kakakin jam’iyyar PNDS Tarayya ya ce tun da Shugaba Issouhou Mahammadou ya fara mulki babu wani dan siyasa ko dan jarida da shugaban ya garkame a gidan kaso da sunan siyasa.
Yaki da cin hanci, da farautar mahandama na daga cikin batutuwan da ke haifar da ce-ce-ku-ce a tsakanin masu sukar lamirin gwamnatin ta Renaissance da masu kare manufofinta.
Saurari karin bayani cikin sauti.
Facebook Forum