Shugaban Ghana Nana Addo Dankwa Akufo-Addo, ya tsawaita matakin rufe kan iyakokin kasar har zuwa nan da karin mako biyu.
Ministan yada labaran kasar, Kojo Oppong Nkrumah ne ya bayyana hakan a shafinsa na Twitter a ranar Asabar.
“Shugaba @NAKuforAddo ya fitar da wani sabon umurni mai lamba EI 66, wanda ya tsawaita matakin rufe kan iyakar kasar zuwa mako biyu.” Shafinsa na Twitter ya ce.
Ya kara da cewa, “umurnin zai fara aiki ne daga 12 dare na ranar 5 ga watan Afrilu, kamar yadda shafin Oppong Nkrumah ya nuna.
Ministan yada labaran ya kuma ce daukan matakin ya zama dole domin a gujewa yada cutar ta COVID-19, yayin da gwamnati za ta mayar da hankalinta kan gwaje-gwajen cutar da bin diddigin masu dauke da ita.
Alkaluman da hukumomin lafiya ke fitarwa na nuni da cewa Ghana na da mutum 205 da suka kamu da cutar sannan wasu biyar sun mutu.
An kuma sallami mutum 31.
Facebook Forum