Yanzu haka dai ana jiran sakamakon gwaje-gwaje na sama da mutane dubu goma sha biyar bayan da aka inganta shirin gwajin. Sakamakon shine zai tantance mataki na gaba da gwamnati zata bi.
Da yake jawabi ga al'ummar kasar akan matakan da suka dauka na dakile yaduwar cutar, Shugaban Ghana Nana Akufo-Addo, ya ce sakamakon gwaje-gwajen shi zai ba gwamnati damar tsawaita dokar hana zirga-zirga ta makwanni biyu ko kuma a dakatar da ita.
Shugaban ya bayyana cewa a cikin matafiya dubu talatin da aka killace, biyar daga cikin su sun kamu da cutar, yayin da aka sallami mutane 800 daga cikin su, sannan ana shirin sallamar mutane 121 daga cikinsu.
Saurari karin bayani cikin sauti daga Ridwan Abbas.
Facebook Forum