A Jamhuriyar Nijar a karon farko wasu daga cikin mutanen da suka kamu da cutar Coronavirus sun samu waraka makonni 2 kenan bayan bullar kwayar cutar ta Covid 19 a kasar.
Wata sanarwar da ma’aikatar kiwon lafiya a kasar ta fitar ne ta bayyana hakan.
A yanzu dai mutum 184 ne suka kamu da cutar a Jamhuriyar Nijar yayin da mutane 10 daga cikinsu suka rasu rayukansu.
A cikin mutum 13 da aka sallama har da wasu fitattun mutane irinsu mataimakin shugaban majalisar dokokin kasar Iro Sani.
Kwanaki kadan bayan barkewar annobar ta covid 19 a Nijar masu amfani da kafafen sada zumunta sun yi ta korafi a game da rashin jin labarin wani dan kasar da ya samu waraka daga wannan cutar, saboda haka bayyanar wannan labari a yau babban albishir ne ga jama’a.
Sanarwar ma’aikatar kiwon lafiyar ta kara da cewa kawo yanzu mutum 161 ne ke kwance a asibiti sanadiyar wannan annoba.
Ministan kiwon lafiya Dr Iliassou Idi Mainassara ya kara tunatar da jama’ar Nijar muhimmancin bai wa likitoci hadin kai don cimma nasarar wannan gagarumin yaki.
Saurari wannan rahoton a sauti.
Facebook Forum