Rahotanni sun nuna cewa hakan ya faru a wurare da dama a gewayen Kampala a yau Alhamis din nan, yayinda ‘yan Uganda ke kada kuri’a a zaben shugaban kasa da na ‘yan majalissa.
Wata wakiliyar muryar Amurka Eliizabeth Paulat ta fadi cewa, jami’an tsaro sun harba barkonon tsohuwar bayan da jama’a suka tunkari wajen ‘yan sanda, suna korafin cewa basu sami damar kada kuri’a ba kuma an dauke akwatinan zabe daga rumfuna kafin cikar lokacin da aka bada.
Da farko dai, hukumar zaben Uganda ta fada a wata sanarwa cewa an fara kada kuri’a akan lokaci a yawancin sassan kasar duk da cewa akwai dan jinkirin da aka samu a wasu sassan babban birnin da kuma gundumar Wakiso.
‘Yan kasar uganda fiye da milayn 15 aka yi wa rijista don kada kuri’a a zaben shugaban kasa da na ‘yan majalissa da kuma na kananan hukumomin da ake yi.