Sauran mako daya ya rage a gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisa a kasar Uganda, wato ranar 18 ga watan Fabarairun nan, kuma dan takarar babbar jam’iyyar adawa ta Forum for Democratic Change, Kizza Besigye, wanda ke da magoya baya da yawa a wajen kemfe da gangamin zabe, ya ce yana fargabar ba masu kada kuri’a cin hanci shine babban kalubalen da zai iya samu.
Besigye ya kara da shugaba Museveni a zabuka 3 da aka yi a baya, a shekarar 2001, da 2006, da kuma 2011.
A farkon makon nan, mai magana da yawun gwamnatin Uganda Ofwono Opondo ya ce Jam’iyyar NRM ce zata kara kada jam’iyyar Besigye “bravado” ranar 18 ga watan fabarairun nan.