Shugabannin kungiyar sunce suna nan suna tattaunawa da kungiyar Yan tawaye domin su bari shugaba Museveni ya shiga cikin muhawarar.
Su kace makasudin wannan muhawaran shine domin ya baiwa masu jefa kuriaar damar sanin wani dan takara ne keda manufofin da ya cancanci samun kuriaar su. Tare da kawo karshen kalubalen da ya addabi kasar tasu.
Abinda muhawarar zai mayar da hankali aka sune manufofin kasar game da hulda da kasashen waje, samar da zaman lafiya a duk fadin kasar, tsaro,kasuwanci tsakaninkasar da sauran kasashe, tare da inganta saka hannun jari.
Yanzu haka dai an gayyaci daukacin yan takarar su 8 kafin zaben na shugaban kasa dana ‘yan majilisa.To sai dai abinda wasu ‘yan kasan ke cewa shine ba mamaki shugaba Yoweri Museveni ya halarci muhawarar kamar yadda yaki zuwa na farkon.