Firayim ministan, Ministan Uganda, Ruhakana Rugunda, ya tabattarwa ‘yan kasar cewa zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokokin kasar da za’ayi gobe Alhamis, za’ayi shi lafiya, a gama shi lafiya, don haka yana kira akan dukkan ‘yan kasar da su fito su jefa kuri’unsu bada fashi ba.
Wannan kalamin nashi yana zuwa ne yayinda wasu ke fara bayyana fargabar cewa kila tashin hankali ya barke a lokacin zaben.
Mai yiuwa ne wannan ba zai rasa nasaba da matakin da ‘yansandan Uganda suka dauka jiya Talata ba, akan madugun ‘yan adawa na kasar, Kizza Besigye na jam’iyyar FDC wanda suka toshewa hanya, suka hana shi gudanarda kyamfen dinsa a wasu unguwanni na birnin Kampala.
Firayim minista Rugunda yace abinda ya faru abin a yi nadama ne, amma ya jadadda cewa bai kamata Besigye da mutanensa su nemi yin taron lacca a tsakiyar birnin na Kampala ba.