Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Wucin Gadi Na Mali Ya Koma Kasar


Dioncounda Traore, daga tsakiya,kakakin majalisa da yayi gudun hijira tareda ministan harkokin wajen Burkina Faso, daga hanun dama, da isarsa birnin Bamako.
Dioncounda Traore, daga tsakiya,kakakin majalisa da yayi gudun hijira tareda ministan harkokin wajen Burkina Faso, daga hanun dama, da isarsa birnin Bamako.

Shugaban riko na kasar Mali, Dioncounda Traore ya isa birnin Bamako, domin rantsuwar kama aiki, bayanda shugabannin soja da sukayi juyin mulki suka amince zasu mika mika mulki ga gwamnatin farar hula.

Shugaban riko na kasar Mali, Dioncounda Traore ya isa birnin Bamako, domin rantsuwar kama aiki, bayanda shugabannin soja da sukayi juyin mulki suka amince zasu mika mika mulki ga gwamnatin farar hula, a wata yarjejeniya da suka cimma da kasashe makwabtan Malin.Jiya Asabar aka bada sanarwar cimma wan nan dai-daito.

Dioncounda Traore wanda shine tsohon kakakin majalisar dokokin kasar, zai rike mukamin shugaban kasa karkashin gwamnatin wucin gadi kamin ayi zabe. Jiya Asabar ya koma Mali daga wani gajeren zaman gudun hijira da yayi a makwabciyar kasa Burkina Faso.

Sakamakon wan nan yarjejeniya wani jami’in Ivory Coast Adama Bitongo yace kungiyar raya arzikin kasashe dake yammacin Afirka ECOWAS ta dage takunkumi da ta azawa Mali, domin tilastawa sojoji su mika mulki hanun farar hula. Ranar jumma’a ce suka cimma yarjejeniyar.

Shugaban Ivory Coast Allasanne Ouattara ne shugaban kungiyar na ECOWAS ahalin yanzu. Haka kuma kungiyar tayi alkawarin zata taimkawa Mali ta yaki ‘yan tawayen abzinawa wadan da suka kama galibin aarewacin kasar, har ma suka ayyana kafa kasarsu mai cin gashin kai.

Shugaban sojoji da sukayi yujin mulkin, Amadou Sonogo, yace sojojin zasu zakuda domin a kafa gwamnatin hada kan kasa, domin samun ECOWAS ta janye takunkumin baki daya da ta azawa kasar d a bata da hanyoyin ruwa.

Jiya Asabar a birnin Bamako, farar hula suka yi cicirindo kan titunan rike da alamomi dake kira a sami zaman lafiya.

XS
SM
MD
LG