Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yan Takarar Shugabancin Amurka Sun Gwabza Muhawara Ta Farko


Jiya ‘yan takaran shugaban kasa a zaben bana a nan Amurka, Hilary Clinton ta Democrats da Donald Trump na jam’iyyar Republicans sun gwabza a muhawarasu ta farko, inda suka tabo muhimman batutuwa da yawa, ciki harda maganar dumamar yanayi da Hilary tace Donald Trump yana dauka kamar raha ce.

Hilary tace Donald Trump ya dauka maganar dumamar yanayi kamar almara ce, ita kuma ta san cewa zance ne na hakika, inda shi kuma yake musanta cewa ya taba yin wannan maganar.

Ko bayan wannan sun tabomaganar harajin da Hilary tace Donald yaki barin a ga harajin da yaker biya. Haka kuma sun caccaki juna kan muhaswara akan ko shnugaban Amurka na yanzu Barack Obama dan Amurka ne na asali da aka haifa a nan, abinda Tgrump ya dade yana cewa ba haka bane. Hilary kuma ta zargi Mr. Trump da cewa yana cin amanar ma’aikatansa, baya biyansu hakkokinsu:

Hilary tace ta hadu da ma’aikatan Mr. Trump da yawa da suka yi mata korafin cewa baya biyansu ladar aiyukkan da suke mishi, ciki harda wani mutum da yace Donald bai biya shi ko anini na hidimar da yayi mishi ba, inda Trump yace watakila mutumen baiyi aikin kirki bane.”

Hilary tace tana jin abokin takaran nata yana ganin laifinta da damarar da ta dauro don wannan muhawarar tasu, inda tace mishi, ai ba ma abida ta shirya wa kamar zama sabuwar shugabar Amurka.”

XS
SM
MD
LG