Yar takarar jami’iyar Democrat Hillary Clinton tace tana bukatar ganin an kara tsawata binciken leken asiri da nufin yaki ta’addanci da shi. Tace masana a cibiyar fasaha ta Amurka zasu iya taimakawa wajen bullo da hanyoyin lura da hira da ake yi a kan yanar gizo tsakanin masu shirya kai hare hare a gurguntar da aniyarsu tun kafin su kai hari.
Yayin gangamin yakin neman zaben shugaban kasar Amurka, dan takarar Republican Donald Trump, ya sake yin kira da tsaurara matakai kan yan ci rani da suke shigowa a Amurka.
Da yake ambaton wadanda suka kai hare haren ta’addanci a Amurka, Trump yace “Hillary Clinton tana son ta kyale dubbun dubatan wadannan mutane su shigo kasar.
Trump yace yan sanda Amurka sun san da dama daga cikin wadannan mutanen, amma suna tsoron daukar mataki a kansu da zai hana su kai hare haren, saboda suna gudun kada a zargesu da nuna wariyar jinsi.
Ita ma Clinton ta yi alkawarin tantance masu shigowa kasar, sai dai tace kasar tana da kayan aiki da zata tinkari yan ta’adda na cikin gida.