Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yan Takarar Neman Shugabancin Amurka Sun Caccaki Junansu


Yan Takarar Shugabancin Amurka
Yan Takarar Shugabancin Amurka

Dan takarar Shugabancin Amurka na jam'iyyar Republican Donald Trump, da ta jam'iyyar Democrat Hillary Clinton, sun caccaki juna jiya Talata, su ka yi ta zargin juna da rashin kwarewar da za ta kai Amurka ga nasara a yaki da kungiyar ISIS.

Trump, hamshakin dan harkar gine-gine, mai kakkausan lafazi, wanda ke takarar mukamin siyasa a karon farko, ya yi zargin cewa Hillary Clinton ta na "bayyana jahilcinta game da barazanar 'yan ta'adda ... kuma wannan ya nuna ba ta cancanci zama Shugabar kasa ba."

Ya gaya ma wasu daliban Kwaleji a jahar North Carolina, wacce muhimmiyar fagen dagar yakin neman zabe ce ga duka 'yan takarar biyu, cewa "Da ta ce adawar da na ke yi da 'yan ta'adda na ingiza abokan gabar, anan mun ga cewa Hillary Clinton ta sake nuna cewa lallai ba ta da cancantar Shugabancin."

Ita ko Hillary Clinton, tsohuwar Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka, wacce ke hankoron zama Shugabar kasar ta farko mace, ranar Litini ta yi zargin cewa kalaman Trump na tsanar Musulmi, sun sa ya zama mai kara iza 'yan ta'adda wajen kara samun magoya baya.

Hillary Clinton ba ta fito yakin neman zabe ba jiya Talata, a yayin da ta ke shirye-shiryen muhawara ta farko da za ta yi da Trump ranar Litini mai zuwa. To amma ta tattauna da masu bayar da shawara kan tsaro na kasar kan hare-haren bam da aka kai New York.

Ta ce hare-haren da aka kai a Amurka na baya-bayan nan sun nuna cewa "Mu na bukatar kwararren Shugabanci mai cike da natsuwa." Ba ta ambaci sunan Trump ba, to amma ta ce, "bai kamata mu harzuka, mu na ta kashedi da daga yatsa ba."

XS
SM
MD
LG