Rundunar ‘yan sandan jihar Edo ta tabbatar da labarin sace daliban da wani ma’aikacin makarantar kere kere da gine gine ta kasa ta ‘National Institute of Construction Technology’ ta garin Uroni da ke karamar hukumar Esan North-East a jihar Edo.
Maharan da ba a san ko su wanene ba, sun kai samame ne da sanyi safiyar yau Laraba kana suka sace wasu dalibai da malamin makarantar da ba a san adadinsu ba zuwa wani wuri da ba a gano ba.
Karin bayani akan: 'Yan Bindiga, Mohammed Adamu Abubakar, jihar Edo, da Najeriya.
Jami’in hulda da jama’a na ‘yan sandan jihar, SP. Bello Kontongs, da ya tabbatar da faruwan lamarin, a Benin City babban birnin jihar, ya ce “gaskiya ne lamarin ya faru, akwai kuma batun garkuwa kana ‘yan sanda na bin diddigin gano inda maharani suke.”
An yi garkuwa da mutane uku ciki har da ma’aikacin makarantar da kuma dalibai guda biyu a cewar kakakin 'yan sandan SP Bello.
Sashen Hausa na Muryar Amurka zai ci gaba da bibiyar wannan labarin kuma zamu baku Karin bayani da zarar an samu.