Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar Sojin Najeriya Ta Nemi Gumi Ya Yi Hattara Da Kalamansa


Babban Hafsan Sojin Kasa, Gen. Attahiru, hagu da Sheikh Ahmad Gumi, dama (Hoto: Instagram).
Babban Hafsan Sojin Kasa, Gen. Attahiru, hagu da Sheikh Ahmad Gumi, dama (Hoto: Instagram).

Rundunar sojon Najeriya ta yi gargadi ga Sheikh Ahmed Gumi da wasu shugabanni da suke bayyana wasu kalamai kan rundunar da su rinka taka tsantsan don kar su zubar da mutunci da kimar ta.

A cikin sanarwar da Birgediya Janar Mohammed Yerima ya rattabawa hannu, rundunar sojan ta ce, taga wani bidiyo da ya ke ta yawo da ya nuna sanannan Malamin addinin Musulinci, Sheikh Ahmed Gumi yana zargin cewa sojojin wadanda ba Musulmi ba ne ke da alhakin kai hare hare kan ‘yan bindiga.

A cikin faifan bidiyon, an ga malamin yana fada wa ‘yan bindigar cewa sojojin da ke hare hare da yawa a kansu ba musulmai ba ne.

Karin bayani akan: Birgediya Janar Mohammed Yerima, Sheikh Ahmed Gumi, Nigeria, da Najeriya.

Ya kuma bayyana cewa ya kamata su sani cewa sojojin sun rabu kashi biyu ne Musulmi da wadanda ba Musulmi ba.

Rundunar ta kara da cewa, duk da yake rundunar sojojin Najeriya ba zata shiga kace nace tare da Sheikh Ahmed Gumi malamin da ake girmamawa ba, yana da mahimmanci ta sake jaddada cewa, rundunar sojan kasa ta Najeriya a matsayin ta na cibiyar tsaro ta kasa ba ta tura sojojinta bisa ga kabila ko addini.

Rundunar ta yi kira ga Sheikh Ahmed Gumi da sauran masu bayyana ra’ayin su rinka taka tsantsan don kada su zubar da mutuncin da kimar daya daga cikin amintattun cibiyoyin kasa domin tozarta ta.

Sheik Ahmed Gumi Tare Da Fulani Yan Bindiga
Sheik Ahmed Gumi Tare Da Fulani Yan Bindiga

Sanarwar rundunar sojon Najeriya ta kara da cewa, zata ta ci gaba da kasancewa abin alfahari ga kasa da kuma kare martabar yankunan wannan babbar kasa.

Kalamai da ke zubar da kima da martabar sojojin Najeriya ba wai suna cutar wa ba ne kadai, amma za su cusa gaba tsakanin ‘yan Najeriya.

Bugu da kari, yawancin ayyukan da rundunar sojojin Najeriya suka gudanar an yi su ne bisa tsananin kiyaye ka’idojin aiki, tsarin aiki da mutunta hakkin dan adam na dan kasa ba tare da nuna wariya ba.

Don haka abin damuwa ne da gangan wani shugaba mai fada a ji zai nemi ya batawa rundunar sojojin Najeriya suna.

Sanawar ta kara da cewa, rundunar sojojin Najeriya za ta yi amfani da wannan dama ta bada shawara ga shugabannin masu bayyana ra’yin su da su kula sosai ya yin da suke bayyana ra’ayin su, bisa la’akari da muhimmancin tabbatar da tsaron kasa, musamman a wannan mawuyacin lokaci da dakaru masu kwazo suka zage damtse a kokarin tunkarar dumbin matsalolin tsaro da ke damun al’ummar mu.

Abin da sojojin ke bukata a yanzu shi ne goyon bayan jama’a don gudanar da aikin su yadda ya kamata bisa tsarin aikin.

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG