Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle, sun ba ‘yan bindigar da ke addabar yankin jihar wa’adin wata biyu su mika wuya ko kuma su fuskanci fushin hukuma.
Gwamna Matawalle ne ya bayyana wannan matsaya da suka cimma da shugaba Buhari a lokacin da yake jawabi kai-tsaye ga al’umar jihar daga fadar gwamnati da ke Gusau a ranar Talata.
Karin bayani akan: Muhammadu Buhari, Jihar Zamfara, Gwamna Matawalle, Nigeria, da Najeriya.
“Shugaban dakarun Najeriya (Buhari), ya amince da wa’adin, wanda zai ba wadannan ‘yan bindiga masu turjiya damar su amince da zaman lafiya, su mika makamansu ga gwamnati.” Matawalle ya ce a cikin jawabin nasa.
Jawabin gwamnan ya biyo bayan wata ziyarar aiki ta kwana hudu da ya kai Abuja don tattaunawa da shugaba Buhari kan halin da ake ciki dangane da matsalar tsaro a jihar.
Ya kuma yi gargadin cewa, gwamnati za ta “murkushe duk wani dan bindiga da ya ki mika wuya a tsakanin wannan wa’adi da aka bayar.”
A cewar gwamnan, gwamnatin tarayya tana shirin tura karin dakaru 6,000 domin taimakawa jihar a yakin da take yi da ‘yan bindigar.
Gwamnan ya bayyana cewa tsarin sulhu da gwamnatinsa ta samar, ya samu nasarori da suka hada da kwace makamai a hannun ‘yan bindigar da suka tuba, karbo daruruwan mutanen da aka yi garkuwa da su, bude kasuwanni da maido da harkokin kasuwanci.
“Duk da cewa muna morar wannan dan kwarya-kwaryan zaman lafiyan saboda sulhun da aka yi, da yawa daga cikin ‘yan bindigar sun ki su bi sahun wannan shiri, sai suka zabi su ci gaba da kai hare-hare tare da aikata wasu muggan ayyuka a yankunanmu.”
Saboda haka, “a matsayin kara kaimin ganin an kawo karshen wadannan munanan ayyuka da ‘yan bindigar suke aikatawa, gwamnatin ta dauki wasu matakai.
"Mun ba ‘yan bindigar wata biyu daga yau (Talata) su zo su rungumi zaman lafiya su mika makamansu ga gwamnati.” Matawalle ya jaddada.
A cikin jawabin nasa, Matawalle ya kuma nuna cewa, gwamnati ta lura akwai mutanen da ke zagon kasa ga wannan shiri a ciki da wajen jihar.
“Sannan mun lura cewa, masu ba da bayanai ga ‘yan bindigar na karuwa, kuma ba a gane irin wannan danyen aiki da suke yi saboda halin oho da mutanenmu ke nunawa.”
Jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya, na daga cikin jihohin da ke fama da matsalar ‘yan bindiga, wadanda ke satar mutane. Jihohin Sokoto da Katsina ma fama da ire-iren wadannan matsaloli.
A baya-bayan nan, gwamnatin tarayya ta saka yankin jihar karkashin dokar hana shawagin jiragen sama baya ga haramta ayyukan hakar ma’adinia da aka yi a jihar.
A makon da ya gabata ne aka sako dalibai mata ‘yan makarantar sakandare ta Jangebe su 279 da wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su bayan da suka kwashe kwana hudu a hannunsu.