‘Yan sanda a kasar Senegal sun yi amani da barkokon tsohuwa yau laraba wajen tarwatsa masu zanga zangar dake adawa da sake tsayawa takarar shugaba Abdoulaye Wade domin wani wa’adin mulki na uku.
Daruruwan masu zanga zanga sun yi kokarin jerin gwano zuwa fadar shugaban kasar dake Dakar, bayanda kungiyoyin hamayya suka yi kira da a kara gudanar da zanga zangar adawa da takarar shugaban kasar. Sai dai ‘yan sanda sun killace hanya suka kuma yi amfani da barkokon tsohuwa wajen tarwatsa masu zanga zangar.
Tun farko, kungiyar hamayya ta M-23 Movement ta lashi takobin yin maci zuwa dandalin ‘yancin kasar dake Dakar duk da barazanar haramta jerin gwanon da ake kyautata zaton gwamnati zata yi. Ma’aikatar harkokin cikin gida ta kasar tace ba za a amince da jerin gwanon ba, ta kuma yi gargadi da cewa za a dauki matakin “kare rayukan al’umma da kaddarorinsu”.
Mr. Wade dan shekaru 85 a duniya zai tsaya takarar ne domin wani wa’adin mulki na uku, duk da iyakar wa’adi biyu da kundin tsarin mulkin kasar ya tanada. Watan jiya, kotu ta yanke hukumci cewa wa’adin mulkin da kundin tsarin ya kayyade bai shafe shi ba sabili da ya fara aiki ne a shekara ta dubu biyu.
Yan takara goma sha uku suke kalubalantar Mr. Wade a zaben da za a gudanar ranar 26 ga wannan watan na Fabrairu, da suka hada da tsofaffin abokan hamaryarshi Macky Sall da Irissa Seck. Za a gudanar da zaben fidda gwani idan wanda ya lashe zaben ya gaza samun sama da rabin kuri’un.
An gudanar da zanga zanga da dama a Dakar tunda aka fara kamfen neman zabe. Jiya Talata, yan sanda suka hana wani gungun matasa wani zaman dirshe a dandalin dake tsakiyar birnin Dakar.