An kammala zaben shugaban kasa da akayi a Senegal, bayan an kwashe makonni ana mummunar tarzoma sakamkon shawarar da shugaban kasa mai ci ya yanke na neman sabon wa’adi na uku.
Tunda da farko a wunin jiya lahadi daruruwan mutane ne suka yiwa shugaban kasa Abdoulaye wade, ihu yayinda yake kada kuri’a a mazabarsa.
Mr. Wade ya fusatadda ‘yan kasar Senegal da dama sabo neman kara wa’adin mulki sama da shekaru 12 da tuni yayi a kasar dake Afirka ta yamma.
Masu hamayya suna zargin matakind a ya dauka ya sabawa doka ganin shi ya sanya hanu kan kwaskwarima da aka yiwa tsarin mulkin kasar a 2001 wadda ya takaita tsawon wa’adi mulki wa’adi biyu kacal.
Kotun tsarin mulki wacce shugaban ne ya nada alkalanta ta yanke hukunci cikin watan jiya cewa garambawul din bai shafi shugaba Wade ba domin dokar ta fara aki ne bayan tuni ya fara shugabancin kasar.
‘Yan takara 13 ne suka kara da shugaba Wade ciki har da mutane biyun da suka rikwe mukamin PM karkashin shugaba Wade.
An kashe akalla mutane shida gabannin zaben a rikicin da ya biyo bayan shwararda Mr. Wade ya yanke na sake takara.