A Senigal ‘Yan sanda sun harba borkono mai sa hawaye domin tarwatsa masu zanga-zanga a babban birnin kasar Dakar, wadanda suke kira ga shugaba Abdoulaye Wade ya fasa shirinsa na neman takara domin yayi mulki wa’adi na uku.
Dubun dubatan ‘yan Senigal, galibinsu matasa, sun kaddamar abinda ake ganin zanga-zanga ta lumana a jiya talata. Amma zuwa dare, zanga zangar ta rikida ta dauki salon tarzoma, inda dalibai suka fara jifar ‘Yan sanda da kona tayoyi, nan da nan kuwa ‘yansandan kwantar da tarzoma suka maida martani.
Masu zanga zanga d a yawa sun bayyana bakin cikin ganin babbar kotun kasar ta yi na’ama da niyyar da shugaba Wade ke dashi na sake takara karo na uku, abinda da dama daga cikinsu suke ganin ya sabawa tsarin mulkin kasar.
Hukuncin kotun ya janyo zanga-zanga a fadin kasar, har aka kashe akalla mutane uku.
An tura gungun ‘Yansandan kwantar da tarzoma wasu cikin motoci masu sulke, an girke su da nufin tabbatar da zaman lafiya lokacin wan nan zanga-zanga.
Babban sakataren majalisar dinkin duniya Ban Ki-moon ya bayyana damuwa kan karin zaman dar dar, gabannin zaben kasar da za a yi cikin watan Febwairu.