Kungiyar Tarayyar Afirka da kuma Tarayyar tattalin Arzikin Afirka ta Yamma, ECOWAS, zasu tura wata tawagar hadin guiwa zuwa kasar Senegal domin ta yi kokarin kawo karshen tashin hankalin da ake yi kafin zaben shugaban kasa na ranar lahadi mai zuwa.
Tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo, shi zai jagoranci tawagar. Darektan yada labarai na kungiyar ECOWAS, Sonny Ugoh, ya fadawa Muryar Amurka cewa duk da mummunar taho-mu-gamar da aka yi a tsakanin masu zanga-zanga da dakarun tsaro, ana iya warware wannan lamari ta hanyar tattaunawa.
Jami’an gwamnati sun ce an kashe mutum jiya lahadi a birnin Kaolack, a yayin da ‘yan sanda suka yi arangama da masu zanga-zangar nuna rashin yarda da sake tsayawa takarar shugaba Abdoulaye Wade a wa’adi na uku.
‘Yan hamayya sun ce Mr. Wade bai cancanci tsayawa takara ba a saboda tsarin mulki ya kayyade wa shugaba wa’adi biyu kawai. Amma a watan da ya shige, kotun kolin Senegal ta ce wannan tanadi na tsarin mulki bai shafi Mr. Wade ba domin yana kan karagar mulki a lokacin da aka fara aiki da shi.
Mutane akalla 6 sun mutu a taho-mu-gamar da aka rika yi kan tituna tun lokacin da kotun ta yanke wannan hukumci.