An girke ‘yan sandan kwantar da tarzoma a duk fadin Dakar babban birnin kasar Senegal inda ake kyautata zaton masu zanga zanga zasu taru domin nuna adawa da sake tsayawa takarar shugaba Abdoulaye Wade domin wani wa’adi shugabanci na uku.
Wata kungiyar hamayya da ake kira M23 ta yi kira da a fito a yi zanga zangar lumana yau Talata. Gwamnati ta bada izinin yin zanga zangar ne ‘yan sa’oi kafin lokacin da aka shirya farawa.
Shaidu sun bayyana babban birnin kasar a matsayin mai cike da damuwa, inda mutane da dama suke maida hankali wajen sauraron labarai yayinda da dama suka kauracewa tsakiyar birnin inda ake kyautata zaton gudanar da zanga zanga.
Shugabannin M23 sun ce sun kira zanga zangar ne domin matsawa shugaban kasar dan shekaru 85 lamba ya janye tsayawa takara.
Ranar jumma’a kotun kundin tsarin mulkin kasar Senegal ta yanke hukumci cewa, shugaban kasar mai ci yanzu yana iya tsayawa takara domin wa’adin shugabanci na uku duk da yake kundin tsarin mulkin kasar ya kayyade wa’adin shugabanci zuwa biyu kadai. Shugaba Wade yace dokar bata shafe shi ba kasancewa an kafa ta bayan zabenshi.