Dubban ‘yan Najeriyar da suka tsere zuwa kasar Chadi domin gujewa rikicin kungiyoyi masu ikrarin jihadi a shiyar arewa maso gabashin kasar sun koma gida bayan shafe fiye da shekaru 10, kamar wani mai magana da yawun wata hukumar bada agaji ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP a yau Laraba.
Kimanin ‘yan gudun hijira 3, 600 ne suka isa Maiduguri, babban birnin yankin a cikin manyan motoci daga garin Baga Sola na kasar Chadi, inda suke zaune tun cikin 2014, a cewar Abdullahi Ibrahim Umar, kakakin hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Borno.
“Mun karbi fiye da ‘yan gudun hijirar da suka dawo daga kasar Chadi 3, 600 tun daga Litinin din da ta gabata, inda adadi mafi yawa ya iso a jiya Talata,” kamar yadda umar ya shaidawa afp.
A bisa yarjejeniya, an tsara dawo da ‘yan gudun hijira 7, 790 da suka nemi dawowa gida bisa radin kansu, a cewar Umar.
Hukumomin jihar Borno sun samar da matsugunan wucin gadi domin sauke ‘yan gudun hijirar da suka dawon gabanin a mayar dasu gidajensu na asali bayan kammala tantancesu, kamar yadda ya kara bayyanawa.
Gwamnatin jihar Borno ce ta dauki nauyin aikin dawo da mutanen gida da hadin gwiwar kasar Chadi da hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (UNHCR), biyo bayan rattaba hannu a kan yarjejeniyar dawo dasu gida a makon daya gabata a lardin Lac na kasar Chadin.
Dandalin Mu Tattauna