Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Adawa A Majalisar Dokokin Nijar Sun Ki Yin Na’am Da Kasafin Kudin 2023


Majalisar Dokokin Kasar Nijar
Majalisar Dokokin Kasar Nijar

Majalisar dokokin Nijar ta yi na’am da kasafin kudaden shekarar 2023 da nufin bai wa gwamnatin kasar cikakkiyar damar gudanar da ayyukan da ta kira na inganta rayuwar al’umma, sai dai ‘yan adawa a majalisar sun juya wa kasafin baya saboda a cewarsu ba a yi la’akkari da halin da kasar ke ciki ba.

NIAMEY, NIGER - Dalilin haka ne mahawara ta kaure a zauren majalisar a cikin daren jiya Laraba lokacin da ake shirin kada kuri’a kan kasafin kudaden na 2023.

Zaman wanda Ministan kudin kasa Dr. Ahmed Djidoud da mukarraban ma’aikatar kudi suka halarta, ya kasance wani lokaci na yi wa kasafin filla-filla, abinda ya sa a karshe ‘yan majalissar suka yi na’am da shi da kuri’u 135 daga cikin wakilai 166.

Rashin gamsuwa da hanyoyin da za a yi amfani da su wajen tattara kudaden da ake bukata da kuma yadda aka yi biris da matsalolin ‘yan kasa a kasafin na 2023 ya sa ‘yan adawa suka yi watsi da shi, a cewar Hon. Moutari Ousmane wanda ‘dan majalissa ne daga jam’iyar RDR Tchanji ta ‘yan adawa.

Tun daga 2015 wato lokacin da Nijar ta tsinci kanta cikin yanayin tabarbarewar tsaro, hukumomin kasar ke tanadin babban kaso na kasafin shekara domin kula da wannan fanni kamar yadda a wanann karon aka ware wa ayyukan tsaro kashi 13 daga cikin 100 na kasafin shekarar mai shirin kamawa matakin da shugaban kungiyar AEC dake bin diddigin kasafin kudin kasa Moussa Tchangari ya ayyana a matsayin wata ragguwar dubara.

Miliiard ko kuma biliyan 3,245 na cfa ne gwamnatin ta Nijar ta kudiri aniyar kashewa domin gudanar da ayyukan kasa a shekarar 2023, kasafin da ya dara na 2022 mai Milliard 2,880 da ‘yan kai yayin da kasasfin 2021 ya kunshi Milliard ko Billion 2,830 da ‘yan kai.

Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:

‘Yan Adawa A Majalisar Dokokin Nijar Sun Ki Yin Na’am Da Kasafin Kudin 2023
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00

XS
SM
MD
LG