Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yawan Nade-Naden Mashawarta A Majalisar Dokokin Kasa Ya Haifar Da Ka-ce Na-Ce A Tsakanin Jama'ar Nijar


Majalisar Dokokin Kasar Nijar.
Majalisar Dokokin Kasar Nijar.

A Jamhuriyar Nijar wasu ‘yan  siyasa da jami’an fafutuka sun fara kiraye-kirayen ganin an dakatar da abin da suke kira facaka da kudaden jama’a.

Lamarin ya biyo bayan bullar wasu bayanai da ke zargin cewa, kakakin majalisar dokokin kasa Seini Oumarou na da mashawarta akalla 1,000 wadanda ke daukan albashi mai tsoka a kowane wata a yayin da kasar da jama’arta ke cikin halin fatara da talauci.

Tun a makwannin da suka gabata ne aka fara guna-guni kan abubuwan da ke faruwa a majalisar dokokin kasa game da yadda ake kashe kudaden majalisar bakatatan inda kakakinta Seini Oumarou ke da mashawarta kusan 1,000 wadanda kowanne daga cikinsu ke karbar 302, 000 na cfa a matsayin albashin wata, Shugaban jam’iyar PJD Hakika Mahaman Hamissou Moumouni kusa a kawancen jam’iyun dake mulkin Nijer ya fasa kwai.

Ya ce kakakin majalisar dokokin kasa Seini Oumarou na da mashawarta sama da 1000 daga cikinsu kujeru 600 kason jam’iyarsa sai Jam’iyar PNDS mai kujeru 250 sannan sauran jam’iyu suka raraba ragowar kujerun a tsakaninsu.

Da farko kowanne daga cikin wadanan mashawarta na samun 402000f a wata to amma tankiyar da aka fuskanta tsakanin PNDS Tarayya da kawarta ta yi sanadin rage masu albashi zuwa 302000f. Shugaba Bazoum ba ya ra’ayin wannan tsari na tara mashawarta ba sabanin yadda masu tafiyar da harakokin jam’iyarsa ke da ra’ayin irin wadanan mukamai na kashe mu raba.

Tuni dai ‘yan rajin kare hakkin jama’a suka yiwa wannan al’amari ca ganin yadda abin ke faruwa a wani lokacin da asusun bital-malin Nijer ke fama da karancin kudade yayinda talakka suka zura wa gwamnati idanu game da matsalolin dake addabar su. Mamba a hadakar kungiyoyin fararen hula na FSCN Abdou Elhadji idi ya yi tur da abinda ya kira almobazarancin da kudaden jama’a.

Muryar Amurka ta nemi jin ta bakin mai magana da yawun kakakin majalisar wato Ousseini Salatou akan wannan dambarwa, sai dai haka ta ba ta cimma ruwa ba domin wayarsa ba ta shiga har izuwa lokacin aika wannan rahoto yayin da a dai bangare mun zanta da wani kakakin PNDS Tarayya Alhaji Assoumana Mahamadou, ya na mai nisantar da jam’iyarsa daga wannan badakala.

A bisa tsarin dokokin Nijar, majalisar dokokin kasa na da cikakken ‘yancin da hurumin gudanar da kasafin kudadenta na shekara wanda a ke ganinsa a matsayin dalilin da ya sa kakakin majalisar na fakewa da wannan damar ne wajen daukan mashawarta masu tarin yawa.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:29 0:00
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Kamala Harris Ta Amince Da Shan Kaye A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Sakamakon Zaben 2024 A Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG