Sai dai jam’iyyun hamayya sun gargadi hukumomi su da dakatar da wannan yunkuri don gabatar da batun a gaban al’uma ta hanyar shirya zaben raba gardama.
A sanarwar da suka fitar akan bukatar da gwamantin Nijar ta gabatar wa majalisar dokokin kasa da nufin samun izinin ba kasashe aminnai damar kafa sansanin soja, shugabannin jam’iyun adawa a karkashin jagorancin tsohon shugaban kasa Mahaman Ousman sun nuna rashin cancantar hanyar da mahukunta ke shirin bi akan wannan batu dake bukatar takatsantsan in ji su.
Dan majalisar dokokin kasa bugo da kari shugaban jam’iyar AMEN AMIN Omar Hamidou Tchana ya ce hukumomi sun bukaci majalissa ta amince da gyaran fuskar tsarin manufofin gwamnati da zimmar boye wa ‘yan majalisa abubuwan dake kunshe cikin yarjejeniyoyin da ta cimma da kasashen dake shirin maido sojojinsu zuwa Nijer.
‘Yan adawar sun bukaci ‘yan kasa kadda su yarda da wannan yunkuri dake da matukar hadari a cewarsu, sannan sun ja gargadi mahukunta su shirya zaben raba gardama a game da wannan shiri.
Ita ma kungiyar tsofaffin ministoci da manyan jami’an gwamnati wato CIRAC a sanarwar da ta fitar ta bayyana rashin gamsuwa da shirin girke dakarun kasashen waje ganin yadda abin ka kiya zamewa baki dayan yankin Afrika ta yamma matsala.
Tsohon ministan cikin gida Idi Ango Omar shi ne shugaban wannan kungiya.
A hirarmu da shi akan wannan magana, tsohon ministan tsaron kasa dan majlisar dokoki Kalla Moutari ya tabbatar da irin tasirin da zuwan sojoji aminnai ka iya yi a yakin da aka sa gaba a yankin sahel.
A yanzu haka kasar Faransa da tuni ta fara kwashe kayanta daga Mali na jiran amsar majalisar dokokin Nijar akan bukatar hijirarta kasar yayin da a makon jiya kasar Jamus ma ta fara nuna alamar neman samun matsugunni don ci gaban abin da ta kira yaki da ta’addanci.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: