Wata cibiyar horar da kwallon kafa ta duniya da ke da mazauninta a Dubai ta tsara gudanar da wani sansanin atisaye na wannan bazara a Najeriya, tare da manufar karfafa wa matasa masu tasowa ta haujin tamaula.
Cibiyar ta Yoshi wadda ke da kokarin zakulo matasa da masu baiwa da hazaka, tare da zimmar karfafa musu gwiwa su sami madogara a rayuwa, ta kammala shirye-shiryen soma sansanin atisayen ne a Abuja babban birnin Najeriya, daga ranar 13 zuwa 27 ga wannan watan na Agusta.
Atisayen zai sami halartar hazikan ‘yan wasan Najeriyar daga ‘yan shekara 14 zuwa 18 da haihuwa, wadanda kuma ake sa ran sansanin zai samar musu dama mai tarin yawa, da ta hada har da inganta rayuwarsu ta kwallon kafa, sada su da kungiyoyin kwallon kafar Turai da kuma jami’an kasuwancin ‘yan wasa.
Wanda ya assasa cibiyar Ahmad Geidam, ya ce an tanadi ingantattun kayayyakin horar da kwallon kafa a sansanin da za a gudanar, haka kuma ya ce za a hada da wani taron fadakarwa ga ‘yan wasa har ma da iyayensu, domin wayar musu da kai kan su kauce wa jami’an kasuwancin ‘yan wasa na bogi da ‘yan damfara.
Gaidam ya ce za a kuma gudanar da wata ‘yar kwarya-kwaryar gasar kwallon kafa a karshen sansanin, inda zakarun gasar za su sami kofi da wasu kyautuka masu yawa, a yayin da kuma za a ba su damar kasancewa membobin cibiyar ta horar da kwallon kafa ta Yoshi.
Dubun dubatar jama’a ne suka taru a birnin London a yau Litinin, domin bikin nasarar da kungiyar kwallon kafar mata ta Ingila ta samu, na lashe babban kofin gasar kwallon kafar mata karon farko a tarihi.
Kasar ta Ingila ta doke dadaddiyar babbar abokiyar adawarta kasar Jamus da ci 2-1, a wasan karshe na gasar kwallon kafar cin kofin nahiyar Turai ta mata ta bana.
‘Yan wasan na Ingila sun bayyana a saman dandamali a gaban dubban jama’ar da suka taru a dandalin Trafalgar a yau Litinin, inda mai horar da su Sarina Wiegman ta daga kofin gasar da suka lashe, lamarin da ya sa dandalin barkewa da sowa da wake-waken murna.
Wannan ne karon farko da Ingila din ta lashe kofin gasar a tarihi, kuma shi ne kofin gasar mata na farko da ta taba lashewa, bayan da ta doke kasar Jamus da ta fi kowace kasa tarihin nasara a gasar, wadda ta lashe har sau 8 a tarihi.
Kungiyar kwallon kafar Bayern Munich ta kasar Jamus ta bayyana cewa ba ta da bukatar sayen ‘yan wasan gaba a halin yanzu, lamarin da ya kawo tarnaki ga yunkurin dan wasan Super Eagles ta Najeriya victor Osimhen na komawa kungiyar.
An yi ta baza rade-radin da ke ta’allaka Osimhen da ke taka leda a kungiyar Napoli da komawa Bayern din, a yayin da kuma ake cewa kungiyar na farautar dan wasan gaba da zai maye gurbin shahararren dan wasanta Robert Lewandowski da ya koma Barcelona ta kasar Spain.
Haka kuma wasu rahotanni sun bayyana cewa kungiyar ta nuna sha’awar sayen Cristiano Ronaldo na Manchester United, da kuma dan wasa Tottenham Harry Kane.
To sai dai shugaban kungiyar ta Bayern Munich, Oliver Kahn ya ce yanzu haka kungiyar ba ta da bukata da ‘yan wasan gaba, kasancewar tana da wasu matasan ‘yan wasa da za su iya cike duk wani gibi da ake ganin akwai a kungiyar.
Saurari rahoton Murtala Faruk Sanyinna: