Hukumar kwallon kafa ta Najeriya NFF ta ce mai horar da ‘yan wasan Super Eagles na Najeriya a mataki na wucin gadi Augustine Eguavoen zai ci gaba da zama a matsayinsa na kocin kungiyar.
A watan Disambar bara, hukumar ta NFF ta sanar da Jose Vitor dos Santos Peseiro a matsayin sabon kocin Super Eagles.
Hakan ya faru ne bayan sallamar Gernot Rohr inda aka nada Augustine Eguavoen a matsayin kocin wucin gadi kafin Peseiro ya karbe shi.
Hukumar ta NFF ta ce Eguavoen zai rike mukamin ne zuwan bayan gasar cin kofin nahiyar Afirka.
Sai dai cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin, NFF din ta ce Eguavoen zai ci gaba da zama a matsayin kocin na wucin gadi.
“A ranar Litinin hukumar kwallon kafar Najeriya ta sanar da yin garanbawul ga manyan mambobin tawagar kungiyar ta maza ta Super Eagles, inda Agustine Eguavoen zai ci gaba da zama a matsayin mai horar da kungiyar a mataki na wucin gadi.” Sanarwar ta ce.
Sai dai sanarwar ba ta ambaci makomar Peseriro ba.
Sanarwar ta kara da cewa, “tsohon zakaran dan wasan Najeriya Emmanuel Amuneke zai zama mataimakin Eguavoen.”
Shi dai Eguavoen ya taka rawar gani a gasar AFCON da aka kammala inda ya kammala wasaninsa uku ba tare da na doke Najeriya ba.
Hasali har kyauta ya lashe ta mai horar da ‘yan wasan da ya fi fice a matakin wasannin rukuni a gasar ta AFCON.