Laftanar Janar Attahiru ya bayyana hakan ne a lokacin da ya nuna wa manema labarai wasu makamai da suka kame a hannun mayakan Boko Haram a garin Marte da Chukun Gudu da wasu kauyuka da kewaye da wadannan yankuna suke a arewacin jihar Borno.
Ya ce duk wani abu da ya kamata a yi wa soja kama daga kayan sawa, wurin kwanansa, makamai da za su yi aiki da su da motocin yakin duk za’a samu a bawa sojojin domin su yi abin da ya kamata, wannan shi yasa ya zo su yi magana baki da baki don jin abin da suke bukata a duba a ba su.
Karin bayani akan: Laftanar Janar Attahiru, Boko Haram, jihar Borno, Nigeria da Najeriya.
Wadannan manya manyan makamai da kanana kananan bindigogi sun tasarma 36 da kuma manyan bindigogi masu kakkabo jiragin sama an bajesu ne ga manema labarai dan nunawa jama'a irin nasarorin da jami’an sojan suke samu a yakin da su ke yi.
Shima a nasa bangare lokacin da ya ke jawabin bankwana ga rundunar Sojan Najeriya ta 7 da ke jihar Borno, tsohon kwamandan rundunar, Mejo Janar Abdul Khalifa Ibrahim, ya yi kira ga sojojoin su ci gaba da zama masu tarbiya da kwazo kuma masu jajircewa.
Ya kuma kara da cewa, su rinka kai hare hare ga mayakan Boko Haram cikin dare saboda mayakan suna son zirga zirga cikin dare don haka dole ku rinka hari cikin dare.
Sai dai a daidai lokacin hada wannan rahoton ake samun wasu rahotanni daga arewacin jihar Borno suna cewa, mayakan Boko Haram sun kai hari, amma har ya zuwa wannan lokaci ba’a samu wani cikakken bayani ba dangane da harin.
Jihar Borno dai ta shafe sama da shekara 10 tana fama da hare haren mayakan kungiyar Boko Haram da suka addabi jihar da suka kashe mutane da dama tare da lalata dukiya mai yawa.
Kungiyar Jama’atu Ahlis Sunna Lidda’awati Wal-Jihad, da aka fi sani da Boko Haram da ake kyautata zaton ta fara hada kan masu tsats-tsaurin ra'ayin addinin Islama ne a garin Maiduguri cikin shekara ta 1999 karkashin jagorancin Mohammed Yusuf, ta kai kazamin hari na farko ne a shekara ta 2003 lokacin da mayaka sama da 200 su ka kai hare hare kan ofisoshin 'yan sanda a jihar Yobe.
A shekara ta 2009 kungiyar ta fara daga hankali a garin Bauchi da nan da nan ya bazu zuwa jihohin Borno, Kano da kuma Yobe. Tun daga wannan lokacin ake fama da hare haren kungiyar musamman a jihohin Borno da Yobe, da kuma wadansu kasashe da ke makwabtaka da Najeriya.
Saurari cikakken rahoton Haruna Dauda Biu: