Rahotanni daga jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya na cewa wasu daruruwan daliban sakandaren jihar sun tsallake rijiya da baya, bayan da wani yunkurin sace su ya gaza samun nasara.
Da safiyar ranar Lahadi wasu 'yan bidinga masu garkuwa da mutane suka kai harin a makarantar sakandaren gwamanati ta kimmiyya, wacce ke karamar hukumar Ikara.
Yayin wani taron manema labarai a ranar Lahadi, kwamishinan tsaro da kula da harkokin cikin gida na jihar Samuel Aruwan, ya fadawa manena labarai cewa, maharan sun mamaye makarantar ne da goshin asubahi, kafin daga bisani sojoji suka je suka fatattake su.
Bayanai sun yi nuni da cewa an yi musayar wuta tsakanin ‘yan bindigar da sojojin wadanda suka samu galaba akan maharan.
A cewar Aruwan, daliban makarantar sun yi amfani da matakan tsaro da aka saka a makarantar don ankarar da jami’an tsaro kan halin da suke ciki, wadanda ba tare da bata lokaci ba suka kai musu dauki.
Hukumomin jihar sun ce dalibai 307 ne a cikin makarantar a lokacin da lamarin ya faru kuma dukkansu suna cikin koshin lafiya.
Wasu majiyoyi sun fadawa Murnar Amurka cewa masu gadin makarantar ne suka yi namijin kokari wajen fatattakar maharan kafin isowar sojojin, inda suka yi amfani da bindigogin gargajiya na harbi-ka-ruga.
Hakan ya sa 'yan bindigar arcewa ba shiri, saboda suna tunanin masu gadin suna dauke da makaman da za su iya kai su kasa.
Wannan hari na zuwa ne yayin da ake kan jimamin sace wasu daliban makarantar kwalejin kula da harkokin gandun daji, wadanda aka sace su a karshen makon nan.
Dalibai kwalejin 39 ne yanzu haka suke hannun masu garkuwa da mutanen.
A ranar Asabar wani hoton bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta wanda ake kyautata zaton maharan ne suka dauka, ya nuna daliban kwalejin suna kuka tare da neman gwamnatin ta kai musu dauki.
A baya, gwamnan jihar Malam Nasiru El Rufai, ya ce gwamnatinsa ba ta da niyyar yin sulhu da 'yan bindiga kamar yadda wasu jihohin yankin yammacin arewacin Najeriya ke yi.
A saurari rahoto cikin sauti daga Isah Lawal Ikara: