Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Aka Kashe Alkali A Jihar Enugun Najeriya


Gwamnan jihar Enugu Lawrence Ifeanyi Ugwuanyi (Twitter/@kwankwasoRM)
Gwamnan jihar Enugu Lawrence Ifeanyi Ugwuanyi (Twitter/@kwankwasoRM)

Bidiyon ya nuna yadda wasu ‘yan bindiga uku dauke da makamai, suka zakulo mutumin daga wata bakar mota suka bindige shi har lahira nan take.

Wani faifan bidiyo mai tsawon dakika 45 da ya karade shafukan sada zumunta, ya nuna yadda wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba, suka harbe wani mutum har lahira a cikin birnin Enugu da ke kudu maso gabashin Najeriya.

Rahotanni da dama sun ce mutumin da ‘yan bindigar suka kashe, tsohon alkali Stanley Nnaji ne, ko da yake hukumomin jihar ba su kai ga tabbatar da hakan ba.

Bidiyon ya nuna yadda wasu ‘yan bindiga uku dauke da makamai, suka zakulo mutumin daga wata bakar mota suka bindige shi har lahira nan take.

Lamarin na faruwa ne a daidai lokacin da kungiyar IPOB da hukumomin Najeriya suka haramta, ta ba da umurnin jama’ar yankin kudu maso gabashi su zauna a gida a ranar Litinin, don tunawa da yakin Biafra.

IPOB na fafutukar kafa kasar Biafra ne, a wani yunkuri na bangarewa daga Najeriya.

Karin bayani akan: Ahmed Gulak, jihar Adamawa, Enugu, Goodluck Jonathan, IPOB, Biafra, Nigeria, da Najeriya.

Wannan kisa na zuwa ne kwana guda bayan da wasu ‘yan bindigar kungiyar ta IPOB suka kashe tsohon mai bai wa tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan shawara kan sha’anin siyasa Ahmed Ali Gulak a birnin Owerri da ke jihar Imo.

Gulak na kan hanyarsa ta zuwa filin jirage ne don komawa Abuja, a lokacin da aka tsare shi aka harbe shi.

A ranar Lahadi rundunar ‘yan sanda jihar Imo ta ce ta kashe maharan da suka kashe Gulak wanda tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Adamawa ne.

XS
SM
MD
LG