Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Wakilan Najeriya Na Shirin Soke Shirin Yi Wa Kasa Hidima Na NYSC


Wasu masu yi wa kasa hidima a Najeriya
Wasu masu yi wa kasa hidima a Najeriya

Majalisar Wakilan Najeriya na shirin yin dokar da za ta soke shirin yi wa kasa hidima, NYSC bisa dalilin tabarbarewar Tsaro a kasar.

Dan Majalisar Wakilai Awaji Inimbek Abiante daga Jihar Ribas shi ya gabatar da kudurin dokar da ke neman soke sashi na 315 karamin sashi na 5 na Kundin Tsarin Mulkin Kasa wanda ya shafi dokar bautar kasa na matasa.

Inimek Abiante ya ambaci rashin tsaro, cin zarafi ta hanyar aikin farko da daliban za su yi da kuma rashin kyakyawan sansanonin wayar da kai.

Dan Majalisan ya bada misalin rashin kula da wani dan bautar kasa da fashewar bam da ya shafe shi a Suleja ta Jihar Neja a shekara 2011,inda ya ce abin bakin ciki ne ganin cewa bayan shekaru da dama da kafuwa, shirin ya gaza cimma burin kafa shi.

Dan Majalisar Wakilai Sada Soli Jibiya ya yi karin haske akan kudurin dokar yana mai cewa ko wane dan majalisa yana da hurumin ya kawo kudurin gyara ko na sauya doka idan yana gani bata yi masa ba sai dai ana ba mutane dama su fadi ra'ayinsu kafin a sauya kowace irin doka.

Sada Soli ya ce dan majalisar daga Jihar Ribas bai fahimci irin yanayin da kasa ke ciki ba shi ne ya rika kawo misalai na rashin tsaro. Sada ya ce akwai kuma kaddara da ya kamata mutum yayi la'akari da shi a duk lokacin da irin haka ya faru.

To sai dai Shugaban Hukumar Kula da shirin yi wa kasa Hidima Janar Shuaibu Ibrahim ya mayar da martani cewa a yanayin yi wa kasa hidima ne kawai matasan ke fahimtar hujjojin zaman tare da cudanya da juna har da ma aurataya. Janar Shuaibu ya kara jaddada bukatar ganin shirin ya samu goyon baya daga wurin al'umma saboda a cigaba da inganta dankon zumunci a tsakanin 'yan kasa a daidai irin wanan lokaci da wasu ke ikirarin ballewa daga kasar.

A lokacin da ya ke nazarin wannan batu, kwararre a fanin kundin tsarin mulkin kasa Barista Mainasara Kogo Umar yana mai cewa sashi na 15 sakin sahi na 2 da na 3 na Kundin tsarin mulki yana cewa wajibi ne ma ga Gwamnati ta rika bada kokari wajen ganin an samu chudedeniya tsakanin al'umman kasa daga sasa dabandaban har da aurataiya domin kasa ta hade ta zama daya, kowa ya zama dangin kowa. Mainasara Umar ya ce dattawan kasa su zage damtse wajen ganin haka ya faru domin kasa ta zama cikin lafiya da walwalar jama'a.

Amma daya cikin dalibai da suka taba yi wa kasa hidima, Mary James ta bada shawara cewa kada a rusa shirin sai dai a dan jinkirtar da shi har zuwa wani lokaci.

Abin jira a gani shi ne yadda wanan doka za ta cigaba da inganta manufofin yi wa kasa hidima da ke tsakanin matasan Najeriya da inganta hadewar kasar a matsayin kasa daya dunkulalla.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00

XS
SM
MD
LG