Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

’Yan Sanda Sun Yi Nasarar Bindige Maharan IPOB Hudu a Imo


'Yan Sandan Najeriya a bakin aiki
'Yan Sandan Najeriya a bakin aiki

Jami’an rundunar ’yan sanda a jihar Imo sun ce sun samu nasarar bindige wasu maharan haramtacciyar kungiyar IPOB, mai fafutukar kafa kasar Biafra, 4 a sabon harin da kungiyar ta kai a jihar kamar yadda rahotanni daga jihar suka bayyana.

’Yan bindigar da ake zargin mayakan kungiyar ne sun gamu da ajalinsu ne a lokacin da suke tsaka da kona ofishin ’yan sandan cihar dake yankin Izombe.

Bala Elkana, wanda shine jami’in hulda da jama’a na rundunar a jira Imo ne ya tabbatar da afkuwar lamarin, inda ya ce, maharan sun kai hari ne a caji ofis na Izombe tsakanin karfe 7 zuwa 10 na dare a ranar Asabar, saidai jami’an ’yan sanda suka fatattake su tare da samun nasarar kashe hudu daga cikinsu, ragowar kuma suka tsere da raunin harbi bindiga.

A halin yanzu dai, jami’an ‘yan sanda na cigaba da bin sawun maharan domin kamo su su fuskanci hukunci daga hukuma.

Wannan harin dai na zuwa ne sa’o’i kadan bayan farmakin da ake zargin kungiyar ta kai caji ofis din yan sandan dake yankin Atta na karamar hukumar Njaba ta Jihar Imo.

A baya-bayan nan dai, ‘yan awaren IPOB masu fafutukar kafa kasar Biafra na ta kai munanan hare-hare kan ofisoshin ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar jami’an tsaro da dama.

Gwamnatin Najeriya dai na yi iya bakin kokarin ta wajen magance matsalolin tsaro a yankunan kasar musamman na yankunan kudu dake kara muni sakamakon fafutukar yan awaren Biafra dake neman kafa kasar Igbo lamarin da wasu 'yan kasa ke ganin gazawar gwamnati ce ke kara sanya kasa cikin munin yanayin tsaron rayuka da dukiyoyi.

Kungiyoyin fararren hula na ta gudanar da zanga-zangar neman kawo karshen matsalolin tsaro, wanda na baya-bayan nan sai da suka mamaye harabar majalisun kasar domin nuna wa gwamnatin kasar tura ta kai bango tare da bayyana cewa, yan kasa zasu fara daukan matakan kare kan su.

XS
SM
MD
LG