Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wutar Daji Na Ci Gaba Da Barna a Jihar California


Wutar daji a jihar California
Wutar daji a jihar California

Wutar daji tana ci gaba da barna a bangarori biyu na jihar California jiya Lahadi, a daidai lokacin da ake harsashen cewa za a fuskanci iska mai karfi .

Kawo yanzu mutane 31 suka rasa rayukansu kuma mai yiwuwa adadin ya karu yayin da ma’aikatan ceton rayuka suka isa yankin da wutar ta lakume. Babban jami’in ‘yan sandan arewacin California ya bayyana cewa, har yanzu ba a san inda mutane dari biyu da ishirin da takwas dake zaune a wurin suke ba.

Dubban mutane sun fice daga gidajensu domin ceton rayukansu, ba tare da sun iya daukar ko allura ba.

Hukumomi sunce an shawo kan kashi ishirin da biyar cikin dari na wutar dajin a daya bangaren California yayinda a daya bangaren kuma aka iya kashe kashi goma cikin dari na wutar kawai.

Sama da ma’aikatan kwana-kwana dubu takwas ne suke kokarin kashe wutar dajin a kudanci da kuma arewacin jihar California. Wutar dajin ta tashi ne sakamakon rashin ruwa da kuma iska mai karfi da ake fuskanta.

Jami’ai sunce wutar dajin ita ce mafi muni a tarihin jihar, kuma ta uku mafi muni a tarihin Amurka.

Facebook Forum

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG