Kamar yadda akasari aka sani, Amurka babbar kasa ce kuma mai matukar karfin tattalin arziki da soji. Don haka ta na da tasiri matuka a siyasa da tattalin arziki da kuma zamantakewar duniya baki daya. Hasali ma, ita ce ta fi bayar da gudunmowa da zarar an samu wani bala’i a wani bangare na duniya. Saboda haka, abin da ya shafi Amurka kusan ya shafi kowa a duniya - au kai tsaye, au a fakaice.
To yau dai ake wasu muhimman zabuka a Amurka na rabin wa’adi, wato da zaben gwamnonin jahohi da na ‘Yan Majalisar Dattawa da ‘Yan Majalisar Wakilai.
Amurka dai na da manyan jam’iyyun siyasa biyu: wato da jam’iyyar masu ra’ayin rikau ko Republican (Rifofilikan) da kuma jam’iyyar masu ra’ayin sassauci ko Democrat (Dimokarat).
Akwai jimlar kujeru 535 a majalisar dokokin tarayyar Amurka. Majalisar Dattawa na da kujeru 100, a yayin da kuma Majalisar Wakiliai ke da kujeru 435.
Bayan wannan zaben manufofin harkokin wajen Amurka za su ta’allaka ne kan irin jam’iyyar da ta yi rinjaye a majalisun dokokin tarayyar nan biyu.
Facebook Forum