An gudanar da zaben ne a kan kujerun majalisar wakilai 435 da wasu kujerun 35 a cikin kujeru 100 na majalisar dattawa da kuma wasu kujerun gwamnonin jihohi 36 cikin jihohin Amurka hamshin. An kuma kada kuri’a kan wadansu batutuwa.
Kusoshin jam’iyar Democrat da dama sun sake lashe zabe da suka hada da Amy Klobuchar ta jihar Minnesota da kuma Elizabeth Warren ta jihar Massachusetts, dukansu ana gani mai yiwuwa su tsaya takarar shugaban kasa a shekara ta dubu biyu da ishirin.
Sai dai ‘yan takarar jam’iyar Democrat a jihohin Indiana da Missouri da kuma North Dakota wadanda ke ci yanzu sun fadi zabe, yayinda ake sauraron sakamakon wani zaben majalisar dattijai mai muhimmanci na jihar Florida tsakanin dan jam’iyar Democrat mai ci Bill Nelson da dan takarar jam’iyar Republican Rick Scott. Dan jam’iyar Republican Ted Cruz ya sha da kyar a fafatawar da suka yi da dan takarar jam’iyar Democrat sabon tauraro a jam’iyar Beto O’Rourke, ya ci gaba da rike kujerar mazabar Kudu maso yammacin Texas.
Da wannan nasarar da jam’iyar Democrat ta samu na kwace ikon majalisar wakilai, bayan samun Karin kujeru 23 da take bukata tayi rinjaye a majalisar, wannan na nufin zasu iya takawa shugaba Donald Trump na jam’iyar Republican birki.
Wannan kuma ya nufin majalisar wakilai zata iya kaddamar da bincike kan gwamnatin Trump.
Facebook Forum