Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ya Sanya Hannu Kan Muhimman Umarnin Zartarwa a Ranar Farko na Wa’adinsa na Biyu


Trump Inauguration
Trump Inauguration

Shugaban Amurka Donald Trump ya sanya hannu kan jerin umarnin zartarwa masu muhimmanci a ranar farko ta wa’adinsa na biyu, inda ya ɗauki matakan da suka shafi shige da fice, sauyin yanayi, haƙƙin Ƙasa, da sauran batutuwan da suka jawo hankalin duniya.

Trump ya fara wa’adinsa na biyu a matsayin Shugaban Ƙasa na 47 a ranar 20 ga Janairu, 2025, a wani biki da aka gudanar a Rotunda na Capitol, Washington, DC, tare da tsohon Shugaban Ƙasa Joe Biden da tsohuwar Mataimakiyar Shugaban Ƙasa Kamala Harris.

Wasu daga cikin umarnin da ya sanya hannu sun cika alƙawarin da ya yi wa magoya bayansa a zaɓen 2024, yayin da wasu matakan, kamar ficewar Amurka daga Majalisar Lafiya ta Duniya (WHO), ba a yi tsammani ba.

Shige da Ficen Ƙasa Da Hakkin Zama Dan Kasa

Shugaba Trump ya sanya hannu kan wasu umarni da suka sauya yadda Amurka ke kula da batun shige da fice a Ƙasa.

• Ya ayyana dokar ta-baci a kan iyakar kudu da Amurka.

• Ya sanar da fara wani babban aikin tarwatsa waɗanda ya kira “ƴan fashin shige da fice,” wanda zai yi amfani da sojoji.

• A cikin ofishin Oval, ya rattaba hannu kan dokar da ta rushe haƙƙin Ƙasa ga duk wanda aka haifa a Amurka, duk da cewa wannan yana cikin kundin tsarin mulki. Matakin na iya fuskantar ƙalubale a kotu.

• Trump ya yi gafara ga wasu daga cikin mutanen da suka shiga harin ranar 6 ga Janairu, 2021 a Capitol.

Soke Dokokin Bambance-Bambance

Trump ya soke wasu umarnin tsohon Shugaban Ƙasa Joe Biden da suka tallafa wa shirye-shiryen daidaito da haɗin kai, musamman waɗanda suka shafi haƙƙin ƴan LGBTQ.

• Ya bayyana cewa daga yanzu, gwamnatin Amurka za ta rinka amfani da jinsi biyu ne kawai: namiji da mace.

Ficewa Daga Yarjejeniyar Paris

Trump ya fitar da Amurka daga yarjejeniyar Paris kan sauyin yanayi, matakin da ya maimaita daga wa’adinsa na farko.

Ƙarfafa Hako Mai

A wani umarni, Shugaban ya ayyana dokar ta-baci kan makamashi, tare da ba da damar ƙara yawan hako mai da iskar gas. Yayin jawabin rantsarwa, ya bayyana cewa: “Za mu hako mai, mu samar da ci gaba!”

Soke Aiki Daga Gida

Trump ya ba da umarni ga ma’aikatan gwamnati su koma ofis a cikar lokaci, inda ya soke damar aiki daga gida da aka amince da ita yayin annobar Covid-19.

Ficewa daga WHO

Shugaban ya fitar da Amurka daga Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), yana mai cewa Amurka tana biyan fiye da yadda China ke bayarwa a ƙungiyar.

Dakatar da Dokar Hana TikTok

Trump ya dakatar da aiwatar da wata doka da ta hana amfani da TikTok a Amurka har na tsawon kwanaki 75. Ya ce dole ne babban kamfanin mamallakin TikTok ya sayar da kaso 50% na hannun jarinsa ga Amurka.

Soke Takunkumin Yammacin Kogin Jordan

Trump ya soke takunkumi da aka sanya kan wasu masu zaune a yankin Yammacin Kogin Jordan da aka zarga da cin zarafin Falasɗinawa, matakin da ya rushe dokar da gwamnatin Biden ta kafa.

Cire Cuba daga Jerin Ƙasashen Ta’addanci

Shugaba Trump ya cire Cuba daga jerin ƙasashen da ke tallafa wa ta’addanci, matakin da ya soke na Biden wanda ya cire sunan ƙasar kwanaki kaɗan kafin Trump ya hau mulki.

Wadannan matakai sun nuna yadda Trump ya fara wa’adinsa na biyu da ƙarfi, tare da aiwatar da manyan sauye-sauye da suka dace da manufofinsa na siyasa.

~Yusufudeen A. Yusuf~

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG