Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata Sabuwar Cuta Tana Hallaka Mutane A Jihar Kano


Gwamnan Jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje
Gwamnan Jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje

Kwamishinan kiwon lafiya na jihar, Aminu Ibrahim-Tsanyawa ne ya tabbatar da haka a wani taron manema labarai.

Likitan ya ce mutanen da suka kamu da sabuwar cutar an shimfide su a asibitoci 25 a fadin jihar.

Ibrahim Tsanyawa ya fada cewa, cutar da aka fara gano ta a ranar goma ga watan Maris, an yi zaton ci ko shan gurbatattun wasu abinci ko abubuwan sha ne suka yi sanadin bullarta.

Ya ce an samu wadanda suka harbu ne a kananan hukumomi 13, an riga da an sallami mutane 101, yayin da wasu 183 ke kwance a asibiti.

Kananan hukumomin da cutar ta shafa sun hada ne da, Dala, Gwale, Kano Municipal, Fage, Ungogo, Kumbotso, Tarauni, Bunkure, Rano, Dawakinjudu, Dawakin Tofa, Gwarzo and Danbatta.

Da yake bada bayani a kan cutar, Ibrahim Tsanyawa, ya ce wata yarinya mai shekaru shida ta kamu da ciwon ciki, tana haraswa kana tana fitsarin jini, bayan ta sha ruwa da aka saya a waje.

Mai sayar da ruwan ya ce ya debo ruwan ne daga wata rijiya a wata makabarta a birnin na Kano.

Ana kuma tunanin akwai abubuwan marmari na sha da kuma nau'ukan gishirin da masana’antu ke amfani da su da ake gani sun janyo cutar.

Ya ce “An dauki samfurin ruwa, da jini da abubuwan sha daban daban domin gudanar da binciken cututtuka da ake samu daga abinci da gubar abinci da zazzabin Lassa, da ciwon shawara da zazzabin cizon sauro da kuma gubar sanadarai daga masana’antu.”

Ibrahim Tsanyawa ya fada cewa ma’aikatar kiwon lafiya na jiran sakamakon gwaje gwaje da ake gudanarwa kafin ta tabbatar da ainihin cutar da kuma abin da ya janyo.

Hukumar kiwon lafiyar tana aiki tare da hukumar abinci da magunguna (NAFDAC) da kuma hukumar kare masu amfani da kayaki ta jiha (KSCPC).

Gwamnatin jihar ta jibge jami’ai kana ta kara kaimi a aikin sa ido a kan kananan hukumomi 44 na jihar domin lura da kayayyakin abinci da na sha da ake zaton su ne suka yi sanadin cutar.

XS
SM
MD
LG