A wani taron manema labarai da kungiyar ta kira a Legas shugabanta Abdulsalam Abubakar yace ba zasu cigaba da zura ido suna kallon yadda jami'an tsaro ke farma Fulani da sunan cewa su ne suke kai hare-hare a gonaki tare da kashe mutane ba.
Kungiyar tayi zargin cewa idan jami'an tsaro suka yi kwakwaran bincike zasu ga cewa akwai alaka tsakanin wadanda suke haddasa rikici a kudancin kasar da 'yan kungiyar Boko Haram.
Shugaban kungiyar, Abdulsalam Abubakar, yace mutane sun gagara gane cewa wannan abun dake faruwa 'yan ta'adan da suka addabi kasar suna iya canza salo irir iri musamman idan aka yi la'akari da yadda Fulani suka saba zama cikin daji shekara da shekaru basu taba samun matsala da kowa ba.
Ban da haka Abubakar yace ba'a taba jin Fulani sun gudu sun bar shanunsu ba saboda rikici sai yanzu. Ke nan 'yan ta'ada da suke shiga kamannin makiyaya su ne suke gudu idan an mayar masu da martani. Yace wannan ya nuna ba Fulani ba ne 'yan ta'ada ne suke sayan shanu suna labewa dasu suna kashe mutane. Irin hakan ya faru a Afghanistan da Somalia da wasu wurare.
Wasu mutaen kudancin kasar su ma suna da irin ra'ayin kungiyar. Wani Mr. Akin Olarewaju yace 'yansanda suna musgunawa Fulani da yawa. Wadanda suke kai hari kan manoman yankin ba Fulanin ainihi ba ne. 'Yan Boko Haram ne suke fakewa da Fulani su aikata ta'adanci.Ya kira gwamnati ta kawo masu doki.
Ga karin bayani.